Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron makoki na tsohon shugaban kasar Zimbabwe Mugabe
2019-09-15 16:41:30        cri

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya rasu a wani asibitin kasar Singapore a ranar 6 ga wannan wata, yana da shekarun 95. Kuma a jiya Asabar, gwamnatin kasar Zimbabwe ta gudanar da taron makokinsa.

A wannan rana, jama'ar kasar Zimbabwe fiye da dubu 10 sun taru a babban filin wasa na kasar dake yammacin birnin Harare don yin ban kwana ga marigayi Mugabe. A wurin taron makokin, shugaban kasar na yanzu Emmerson Mnangagwa ya yi jawabi, inda ya bayyana Mugabe a matsayin dan siyasa da jagorin 'yantar da kabilun Afirka. Kana ya ce rasuwarsa babbar hasara ce ga kasar Zimbabwe har ma ga dukkan Afirka. Ya yi kira ga jama'ar kasar Zimbabwe da su yada tunani da akidun marigayi Mugabe da sa kaimi ga raya kasa.

Tsohon shugaban kasar Zambiya mai shekaru 95 Kenneth Kaunda da tsohon shugaban kasar Namibia mai shekaru 90 Sam Njoma da sauran shugabannin kasashen Afirka fiye da 10 sun halarci taron makokin.

An ce, za a binne gawar marigayi Mugabe a makabartar jaruman kasar Zimbabwe. Amma gwamnatin kasar tana shirin gina masa kabari na musamman, har zuwa yanzu ba a tabbatar da lokacin binne shi ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China