Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen Zimbabwe sun gaza fara aiki da sabbin takardun kudin kasar
2019-11-12 10:18:20        cri
Al'ummar kasar Zimbabwe ba su samu damar fara aiki da sabbin takardun kudin kasar ba wanda babban bankin kasar ya alkawarta musu cewa za su fara yawo a tsakanin al'umma tun a ranar Litinin.

Wani gajeren bincike da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi a Harare ya nuna cewa, sabbin kudaden wadanda aka jima ana zumudin fara amfani da su da suka hada da dala biyu na sulalla, dala biyu na takarda, da kuma dala 5 na takarda mutanen kasar Zimbabwe ba su samu damar fara ta'ammali da su a bankunan kasar ba har zuwa karshen ranar Litinin.

Wasu bankunan kasar, da masu hada hadar kudade ta wayar hannu da masu canjin kudaden kasashen waje sun tabbatar da cewa ba su samu sabbin kudaden na takarda da sulalla ba.

A watan jiya gwamnan babban bankin kasar Zimbabwe John Mangudya, ya sanar cewa za'a fara amfani da sabbin takardun kudaden domin saukakawa al'ummar kasar daga halin karancin takardun kudade da ake fuskanta a kasar.

Ya ce sabbin takardun kudade wadanda yawansu ya kai dalar Zimbabwe biliyan 1 zai fara bazuwa sannu a hankali don taimakawa tattalin arzikin kasar nan da watanni shida masu zuwa domin rage yawan hawa-hawan farashin kayayyakin a kasar.

Sabbin takardun kudaden ana sa ran za su fara yawo tare da maye gurbin takardun kudin kasar da aka bullo da su a shekarar 2016.

Zimbabwe ta dauki tsawon lokaci tana fuskantar karancin kudade, lamarin da ya haifar da wasu mutane ke sayar da takardun kudaden da suke dasu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China