![]() |
|
2019-09-15 16:40:53 cri |
A yayin ziyararsa a kasar Zimbabwe, Mr Gu ya gana da shugaban kasar Mnangagwa, inda ya bayyana cewa, marigayi Mugabe dan siyasa ne da ya jagoranci 'yantar da al'ummar kasar, da samar da gudummawa sosai wajen sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, da kuma tsakanin Afirka da Sin baki daya. Ya ce, kasar Sin ba za ta manta da wannan aboki ba. Kana Sin na son hada hannu da kasar Zimbabwe wajen sa kaimi ga raya dangantakar abota ta hadin gwiwa dake tsakaninsu a dukkan fannoni.
A nasa bangare, shugaba Mnangagwa ya bayyana cewa, tara manzon musamman da shugaba Xi Jinping ya yi don halartar taron makokin Mugabe, ya shaida cewa, akwai sada zumunci mai karfi tsakanin jama'ar kasashen biyu, kuma kasarsa za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a nan gaba. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China