Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An binne tsohon shugaban kasar Zimbabwe a mahaifarsa
2019-09-29 16:59:53        cri

An binne tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, jiya Asabar, a mahaifarsa ta Zvimba dake lardin Mashonaland na yammacin kasar.

Sai dai, Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa bai halarci bikin binne magabaci nasa ba, amma Ministar kula da harkokin Larduna ta yammacin Mashonaland, Mary Mliswa-Chikoka ta wakilici gwamnatin kasar.

Da farko, gwamnatin ta nemi iyalan marigayin su binne shi a makabartan gwarazan kasar dake birnin Harare, inda suka amince, har aka gina masa kabari a can.

Marigayi Robert Mugabe ya mutu ne a ranar 6 ga watan a wani asibiti dake kasar Singapore. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China