Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasashen BRICS na son ganin hadin gwiwar kasashen ya karfafa
2019-11-14 13:55:45        cri

 

Tsakanin ranekun 13 zuwa 14 ga watan Nuwamban da muke ciki, ana gudanar da taron ganawa karo na 11 na shugabannin kasashen kungiyar BRICS, wato su Brazil, da Rasha, da India, da Sin, da kuma Afirka ta Kudu, a kasar Brazil. Lamarin da ya sa ake sa ran ganin hadin gwiwar dake tsakaninsu ta karfafu. Yayin da a nasu bangaren, wasu kamfanonin kasashen BRICS ke bayyana burinsu na yin amfani da wannan dama wajen raya harkokinsu.

A kwanakin baya, a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, an yi taron CIIE karo na biyu, wato taron baje kolin kayayyakin da kasar Sin ke shigowa da su daga ketare, inda aka samu kamfanoni daga kasashen BRICS da dama, wadanda su ma suka halarci taron don baje kayayyakinsu.

Hakika kasar Brazil ita ce kasa ta farko, tsakanin kasashen nahiyar Latin Amurka, da ta fara kulla huldar abokai bisa manyan tsare-tsare tare da kasar Sin. Yayin da kasar Sin a nata bangare, ta kasance kasar da ta fi ciniki da Brazil, gami da karbar mafi yawan kayayyakin da kasar Brazil take fitarwa.

A bara, yawan darajar kayayyakin da aka yi cinikinsu tsakanin Sin da Brazil ya zarce dalar Amurka biliyan 100. Sa'an nan, a wajen taron baje kolin CIIE, an ga yadda dimbin yawan 'yan kasuwa Sinawa suka yi layin sayen kayayyaki a wuraren da aka yi baje kolin waken gahawa, da giyar rake, da naman shanu, da sauran wasu abubuwa, duk daga kasar Brazil. A nashi bangare, Thomas Sanoto, darektan sashin kasa da kasa na hadaddiyar kungiyar raya masana'antu ta jihar Sao Paulo ta kasar Brazil, ya ce, "Wannan taron ya nuna ma duniya cewa, ban da fitar da kayayyakinta, kasar Sin na son shigo da kayayyaki daga sauran kasashe. Yanzu a kasarmu ta Brazil, ko da masu samar da ruwan zuma, da nau'o'in gyada ma sun fara sayar da kayayyakinsu a kasuwannin kasar Sin."

Kasar India ita ma daya ce daga cikin kasashen BRICS, wadda ta yi suna a fannin samar da nau'o'in abinci, da kuma al'adu masu ban sha'awa. Hemant Motwani, shi ne shugaban wani kamfanin sarrafa abinci na kasar India, ya gaya ma wakilinmu cewa, "Mun zo nan don habaka kasuwanni, gami da neman damar hadin gwiwa da sauran kamfanoni. Mun san taron CIIE wani dandali ne mai muhimmanci, musamman ma a fannin fitar da kayayyaki zuwa ga kasar Sin. Sa'an nan muna fatan neman damar habaka ayyukanmu tare da abokanmu Sinawa."

Daya daga cikin rumfunan kasashe daban daban da suka samu karbuwa matuka wajen taron CIIE na wannan karo ita ce rumfa ta kasar Rasha, inda jama'a suka nuna sha'awa sosai ga ingantattun motoci kirar kasar. Sa'an nan abincin kasar Rasha da aka nuna, su ma sun janyo hankalin Sinawa sosai. Wani ma'aikacin kamfanin Laycy Queen mai samar da abinci na kasar Rasha, ya gaya ma wakilinmu cewa,

"Muna da sha'awa sosai kan kasuwannin kasar Sin, kuma muna son bude kantunanmu a kasar. Yanzu mun riga mun kulla hulda da wasu kamfanonin Sin da za su sayar da kayayyakinmu a kasar."

Afirka ta Kudu ita ce tattalin arziki na biyu mafi girma a nahiyar Afirka, kana tsakanin kasashen Afirka, ita ce ta fi yin ciniki da kasar Sin, cikin shekaru 9 a jere. Babban darektan hadaddiyar kungiyar sarrafa gangar ruwa wato saholami ta kasar Afirka ta Kudu, mista Muzi Manzi, ya ce,

"Kasuwannin kasar Sin suna da girma, inda ake samun dimbin damammaki na ciniki. Ina fatan samun abokan da za mu iya hadin gwiwa da su a nan kasar Sin, ta yadda za mu sayar musu ingantattun kayayyakin saholami na kasar Afirka ta Kudu."

A shekarun baya, huldar hadin kai tsakanin kasashen BRICS na kara karfafa. Sa'an nan a bara, adadin tattalin arzikin kasashen BRICS ya kai kashi 23.52% na tattalin arzikin daukacin duniya. Wadannan kasashe, wato Brazil, da Rasha, da India, da Sin, da kuma Afirka ta Kudu, na kara taka muhimmiyar rawa a kokarin tabbatar da karuwar tattalin arzikin duniya, da inganta ayyukan kula da duniya, gami da neman wanzar da huldar daidaiwa-daida tsakani kasashe daban daban. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China