Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha zata harba tauraron dan adam na farko a watan Disamba tare da taimakon kasar Sin
2019-10-08 11:11:41        cri
Shugaban kasar Habasha Sahle-Work Zewde, ya sanar a jiya Litinin cewa kasarsa zata harba tauraron dan adam irinsa na farko a tarihi a watan Disambar wannan shekara tare da taimakon gwamnatin kasar Sin.

A cewar shugaba Zewde, gwamnatin kasar Habasha ta yi hasashen cewa idan shirin harba tauraron dan adam din nata ya kai ga nasara, zai taimakawa yunkurin kasar ta gabashin Afrika na zamanantar da fannin aikin gonar kasar.

Shugaba Zewde ya fadawa zauren majalisun dokokin kasar biyu cewa, tauraron dan adam din zai samar da dukkan muhimman bayanan da ake bukata wadanda suka shafi sauyin yanayi, da batutuwan da suka shafi hasashen yanayi, wadanda kasar zata yi amfani da su wajen cimma muhimman burikanta a fannin habaka aikin gona, da raya gandun daji, har ma da fannin kiyaye albarkatun kasa.

Tauraron dan adam din, wadda aka shirya harbawa daga kasar Sin, babbar cibiyar sadarwarta tana yankin kula da kayayyakin sararin samaniya dake Entoto na kasar Habasha, ita ce kadai cibiyar kula da kayayyakin sararin samaniya a kasar ta gabashin Afrika wanda ke dutsen Entoto a wajen Addis Ababa babban birnin kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China