Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta jinjinawa hadin gwiwar majalissar da kungiyar AU
2019-10-31 10:03:06        cri
Babbar jami'ar ofishin MDD dake kungiyar AU, kuma wakiliyar babban magatakardar majalissar a kungiyar Hanna Tetteh, ta ce hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar AU na ci gaba da fadada, musamman a fannonin wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Hanna Tetteh ta ce, sassan biyu na karfafar juna, domin cimma moriya a fannin tsaro da wanzar da ci gaba. A cewar jami'ar, MDD da kungiyar AU sun sanya hannu a ayyukan hadin gwiwar karfafa zaman lafiya da tsaro tun daga shekarar 2017. Kaza lika sassan biyu sun aiwatar da ayyukan tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasashen Afirka da dama, wadanda suka hada da Madagascar, da Janhuriyar Afirka ta tsakiya, da Sudan, da Somalia da kuma kasar Mali. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China