Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin CIIE zai inganta bunkasuwar kasa da kasa cikin hadin gwiwa
2019-11-11 14:42:45        cri
A jiya Lahadi ne aka rufe bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na biyu a birnin Shanghai na kasar Sin. Cikin wadannan kwanaki shida, gaba daya akwai kasashe, da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa guda 181 da suka halarci bikin. Kamfanoni guda dubu 3 da dari 8 kuma sun zo bikin, yayin da 'yan kasuwa na kasa da kasa sama da dubu dari 5 suka halarci tattaunawar ciniki a bikin.

Haka kuma, darajar yarjejeniyoyin cinikin da aka kulla a yayin bikin karo na biyu ya kai dallar Amurka biliyan saba'in da daya da miliyan dari daya da talatin, adadin da ya karu da 23% idan aka kwatanta da na bikin karo na farko. A sa'i daya kuma, ya zuwa yanzu, an riga an sami kamfanoni sama da 230, wadanda suka yi rajistar shiga bikin baje kolin CIIE karo na 3.

Wadannan sakamakon da aka samu ya nuna nasarar da aka cimma ta fuskar inganta hadin gwiwar kasa da kasa cikin dandalin da kasar Sin ta kafa. Lamarin da zai karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin tattalin arziki, tare da neman ci gaba tare.

Da farko, bikin CIIE ya karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin ciniki, da kuma raya tattalin arzikin duniya, ta hanyar kara cinikayyar hajoji da aikin hidima a tsakaninsu. Sa'an nan, ta hanyar yin mu'amala a yayin bikin, an nuna adawa da ra'ayin kariyar ciniki, da kuma goyon bayan da ake yi wa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin tattalin arziki. A karshe dai, an karfafa ra'ayin hadin gwiwa a yayin bikin, wanda ya kasance abin koyi kan yadda za a raya dunkulewar kasa da kasa.

Bikin CIIE da aka yi a birnin Shanghai ya nunawa manyan kasuwannin kasar Sin ga kasashen duniya, da kuma manyan bukatun al'ummar kasa kan harkokin saye da sayarwa. Haka kuma, ya nuna aniyar kasar Sin wajen kara bude kofa ga waje, da goyon bayan kasa da kasa wajen yin hadin gwiwar tattalin arziki, da kuma yin ciniki cikin 'yanci. Sabo da haka, masu halartar taron sun cimma ra'ayi daya kan ra'ayin "babu rufe bikin CIIE, kuma za a zo bikin a ko wace shekara". (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China