Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rana ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya
2019-11-04 17:07:37        cri

Gobe Talata 5 ga watan Nuwamba shekarar 2019, ake sa ran za a bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyu a birnin Shanghai na kasar Sin, haka na tabbatar da cewa, "Rana aka ce ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya"

Mahukuntan kasar Sin shirya tsaf don bude wannan gagarumin biki, kana hankalin duniya baki daya, ya kartata ga bikin na CIIE, kuma saboda girma da ingancinsa da sabbin abubuwan da aka tanada, ya sa ba kowa ne zai samu shiga bikin ba. Wannan ya nuna cewa, managartan matakai da manufofin da kasar Sin take dauka a bangaren cinikayya da zuba jari, sun kara janyo hankulan kamfanoni da 'yan kasuwa daga sassan duniya zuwa babbar kasuwar kasar Sin, da ma kokarin ganin sun halarci bikin baje kolin na CIIE. Idan kana da kyau, aka ce ka kara da wanka.

Yanzu haka, kamfanoni sama da dubu 3 daga kasashe da yankuna sama da 150 sun bayyana aniyarsu ta halartar bikin baje kolin, daga cikinsu akwai kamfanonin kasashen waje fiye da dubu 1 wadanda suka halarci bikin na farko.

Idan aka kwatanta da bikin na bara, a bana, fadin yankunan nune-nune da adadin kayayyakin da za a nuna, da kuma yawan kamfanonin da za su halarci biki, dukkansu sun karu. Bana fadin yankunan nune-nune, ya karu zuwa murabba'in mita dubu 300 daga murabba'in mita dubu 270 na shekarar 2018. Sa'an nan, a fannin karfin kamfanonin da suka halarci bikin a shekarar 2018, kamfanoni 220 dake cikin jerin manyan kamfanonin kasa da kasa guda dari 5 ne, suka halarci bikin, amma bana, adadin ya karu zuwa 250. Bugu da kari, bisa hasashen da aka yi, adadin sabbin kayayyaki da fasahohin da za a nuna a biki na bana, zai wuce na bikin farko.

Wannan ya tabbatar da cewa, nasarar da aka samu a bikin baje kolin da aka shirya a karon farko, gami da matakai da manufofi da kasar Sin take dauka a bangaren harkokin kasuwanci da zuba jari, su ne suka haifar da ingancin bikin na wannan karo, abin da malam Bahaushe ke cewa, gaskiya ba ta neman ado.

Duk da koma bayan da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, kasashen duniya na kokarin shiga kasuwar kasar Sin, don cin gajiyar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin. Musamman ma a halin yanzu da ake fuskantar manufar bangaranci da kariyar ciniki, da tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya da zuba jari ke fuskanta, kasuwar Sin mai salon bude kofa na samar musu da damammaki masu dimbin yawa. Mashartan na bayyana kasar Sin a matsayin sahihiyar kawa da ke son kawo ci gaba da zaman lafiya a duniya, bikin baje koli na CIIE ya zama wata alama dake bayyana yadda Sin take gudanar da manufar bude kofa ga ketare, ya kuma nunawa duniya niyyar kasar Sin na nacewa ga manufar kasancewar bangarori daban-daban da ingiza ciniki maras shinge. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China