Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin inganta shugabanci a birane
2019-11-04 11:17:11        cri

Shugaban kasar Xi Jinping, kuma sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, ya jaddada muhimmanci inganta karfin shugabanci da zamanantar da birane.

Xi Jinping wanda kuma shi ne shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana hakan ne yayin rangadin da ya yi a birnin Shanghai, cibiyar hada-hadar tattalin arziki ta kasar , daga ranar Asabar zuwa Lahadi.

Yayin ziyarar rangadin, shugaba Xi Jinping, ya kuma jaddada bukatar nazari da aiwatar da tunanin taro na 4 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19 da girmama manufar neman ci gaba yayin da ake tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da aiwatar da sabbin dabarun samun ci gaba da gaggauta bude kofa da gyare-gyare da raya tattalin arziki irin na zamani.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China