Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe masu rangwamen wadata sun yi rawar gani a bikin baje kolin CIIE
2019-11-08 20:38:19        cri
Mataimakin daraktan hukumar shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu dake gudana yanzu haka a birnin Shanghai na nan kasar Sin Liu Fuxue, ya shaidawa wani taron manema labarai a Juma'ar nan cewa, bikin na bana ya samu halartar wakilai da dama daga kasashe masu rangwamen wadata.

Liu ya ce sama da kamfanoni 170 daga irin wadannan kasashe 40 ne suka baje hajojin su. Cikin rukunin wadannan kasashe kuwa har da Bangladesh, da tsibirin Madagascar, da Rwanda da Zambia. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China