Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana sayar da kayayyakin Afirka a bikin CIIE
2019-11-08 19:52:24        cri

Sakamakon bukatun masaya iri-iri a nan kasar Sin, ana sayar da kayayyakin da suka fito daga nahiyar Afirka da dama, yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu.

A wannan karo an sayar da karin kayayyakin Afirka da ake shigowa da su kasar Sin, kasancewar bikin CIIE da ake yi a birnin Shanghai na kasar SIn, ba kawai ya raya harkokin cinikin dake tsakanin Sin da Afirka ba, har ma ya samar wa kasashen Afirka karin guraben aikin yi.

Kamar yadda ministan harkokin kasuwanci da ciniki da masana'antu na kasar Zambia Christopher Yaluma ya bayyana, cewar bikin CIIE ya bude wata sabuwar hanya ga kasashen Afirka ta raya tattalin arzikinsu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China