Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna adawa da tsokacin Mike Pompeo game da kalamansa na nuna rashin dacewar tsarin siyasar Sin
2019-11-08 19:33:47        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Juma'a cewa, sau da dama ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, na zargin cewa tsarin siyasar kasar Sin bai dace ba, a cewarsa wai "Sin na haifarwa kasa da kasa kalubale".

Kalaman nasa dai na nuna bin ra'ayin kashin kai, kuma ko kadan kasar Sin ba za ta yarda da wannan zargi na jami'in Amurkan ba.

Haka kuma, Geng Shuang ya ce, Mike Pompeo ya yi hakan ne, domin cimma moriya a fannin siyasa, ta hanyar nuna adawa da kasar Sin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China