Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nuna shakku kan kididdigar tattalin arzikin Sin ba tare da wata hujja ba
2019-10-23 20:54:50        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta ce, wasu mutane suna shakku kan kididdigar tattalin arzikin kasar Sin, ba tare da kwararan shaidu ba.

Hua ta bayyana haka ne a gun taron manema labaru da aka shirya a yau Laraba, inda ta jaddada cewa, game da batutuwan yanayin tattalin arziki da kasar Sin ke ciki, da gudummowar da take bayarwa kan tattalin arzikin duniya, kasashen duniya sun riga sun yanke shawara bisa hakikanin halin da ake ciki. Bata sunan wata kasa ba zai taimakawa wajen warware matsalolin da kasar ita kanta ke fuskanta ba.

Rahotanni na cewa, wani jagoran bangaren Amurka a ranar 21 ga wata ya yi jawabi a yayin taron majalisar zartarwar kasar cewa, kasar Sin na fatan cimma yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya, yanzu tattalin arzikin kasar Sin na cikin wani yanayin da ya fi muni a cikin shekaru 57 da suka gabata, mai yiwuwa ne kuma ci gabansa zai ragu, wannan zai taimaka wajen cimma yarjejeniyar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China