![]() |
|
2019-11-05 11:02:59 cri |
Hukumar wadda ke da alhakin yin gargadi game da ambaliyar ruwa, ta fitar gargadi na matakin karshe ga jihohin da suka hada da Edo da Delta da Anambra da Rivers da kuma Bayelsa.
Darakta Janar na hukumar Clement Onyeaso Nze, ya bukaci hukumomi a jihohin 5, su lalubo al'ummomin dake iyaka da kogin Niger tare da gudanar da shirye-shiryen ko ta kwana. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China