Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta tsawaita wa'adin rufe kan iyakokinta da makwabtan kasashe
2019-11-04 13:49:29        cri

Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar tsawaita wa'adin rufe kan iyakokinta har zuwa farkon shekara mai zuwa, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi.

Kwantirolan hukumar kwastom NCS, mai kula da aiwatar da dokoki na kasar, Victor Dimka, ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita lokacin ci gaba da rufe kan iyakokin kasar har zuwa ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2020.

Dimka, wanda ya sanya hannu kan takardar, ya ce matakin ya haifar da samun nasarori masu tarin yawa idan aka yi la'akari da alfanun da kasar ta samu ta fuskar tsaron kasa da ci gaban tattalin arziki.

Kasar ta yammacin Afrika ta rufe kan iyakokinta da kasashen dake makwabtaka da ita ne a watan Oktoba, makonni kadan bayan da kasar ta gudanar da wani shirin tsaron kan iyakokinta wanda ya shafi bangarori daban daban cikin watan Agusta.

Dimka ya ce, hukumar NCS ya lura cewa, akwai muhimman abubuwan da ba'a kai ga cimma su ba har yanzu, lamarin da tilasta kasar tsawaita wa'adin.

Shirin tsaron kan iyakokin kasar da aka gudanar a watan Agusta, mai taken "Ex-Swift Response," na hadin gwiwa ne tsakanin jami'an kwastam, da na shigi da fici, da 'yan sanda, da kuma jami'an sojoji, wanda ofishin babban mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin tsaro ya shirya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China