Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin jihar Lagos ta Najeriya ta ba Sinawa masu zuba jari tabbacin samun damarmakin kasuwanci
2019-11-05 09:21:07        cri

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, ya ba Sinawa masu zuba jari tabbacin samun dimbin damarmakin kasuwanci dake akwai a jihar, wadanda za su amfani Nijeriya da kasar Sin.

Sanwo-Olu, ya bayyana haka ne, lokacin da yake kaddamar da rumfar kasar Sin a taron baje kolin kasa da kasa na shekarar 2019 dake gudana a jihar ta Lagos, cibiyar hada-hadar tattalin arziki ta kasar.

Sama da 'yan kasar da baki 2000 ne ke baje hajojinsu a taron baje kolin karo na 33 mai taken "hada kasuwancin, samarwa kayayyaki daraja".

Gwamnan ya ce, jihar Lagos na da babbar kasuwa, yana mai cewa, jihar na iya zama cibiyar kawa da fasaha, idan aka samu masu zuba jari da suka dace.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin raya kasuwanci ta hanyar aiwatar da dabaru da samar da kayayyakin more rayuwa.

A nasa bangaren, jami'in dake kula da harkokin cinikayya na ofishin jakadancin kasar Sin dake Lagos, Liu Junsheng, ya ce kasar Sin ta baje kayayyaki a bangarori 4 da suka hada da na masaku da kayayyakin amfanin gida da kayayyakin gyara da kuma kayayyakin da suka shafi inji da laturoni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China