Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun sako 'yan makarantar da suka yi garkuwa da su a Najeriya
2019-10-27 15:12:13        cri

Jiya Asabar jami'ai a Najeriya sun tabbatar cewa, 'yan bindiga sun sako wasu dalibai mata 'yan makaranta su 6 da malamansu biyu na kwalejin Engravers dake yankin Kakau Daji a jihar Kaduna dake arewacin kasar wadanda suka yi garkuwa da su.

Hakan ya faru ne kwanaki 23 da suka wuce bayan da wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai da ake kyautata zato masu garkuwa ne suka yi awon gaba da dalibai da malaman kwalejin biyu.

An sako daliban da kuma ma'aikatan biyu bayan da aka biya kudi kimanin naira miliyan 13.6 kwatankwacin dala 37,621 a matsayin kudin fansa, a cewar jami'in yankin, wanda ya bukaci a sakaye sunansa tun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Majiyar ta kara da cewa, tun a ranar 3 ga watan Oktoba ne aka yi garkuwa da daliban tare da malamansu, inda masu garkuwar suka sako su da sanyin safiyar ranar Asabar da ta gabata.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China