Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 18 a tsakiyar Najeriya
2019-10-24 09:59:45        cri

Wani jami'i a Najeriya ya ce, mutane 18 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa wanda aka samu sanadiyyar ruwan sama babu kakkautawa a tsakiyar Najeriya.

Da yake tabbatar da alkaluman ga manema labarai, Ibrahim Inga, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Nija dake shiyyar tsakiyar Najeriya ya ce, kawo yanzu, mutane 41,959 ne suka kauracewar gidajensu sakamakon annobar.

Hukumar hasashen ruwan sama ta kasar, wacce ita ce ke da alhakin bayar da gargadi game da hasashen ruwan sama a kasar, a wannan shekarar ta yi gargadin cewa, jihohi 36 da babban birnin kasar Abuja ne za su fuskanci ambaliyar ruwan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China