Ba kowa ne zai samu shiga CIIE ba, kasuwar Sin na da makoma mai kyau fiye da hasashen da aka yi
Babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG ya rubuta wani sharhi mai taken "Ba kowa ne zai samu shiga CIIE ba, kasuwar Sin na da makoma mai kyau fiye da hasashen da aka yi", inda aka nuna cewa, za a bude bikin kolin baje kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu a birnin Shanghai ran 5 ga wata. Saboda nasara da aka samu a bikin baje kolin aka shirya a karon farko, yanzu ana zura ido kwarai kan bikin na wannan karo, kasashe da kamfanoni da kuma kayayyakin da za a baje a biki na wannan karo ya zarce na karon da ya gabata, hakan ya sa aka kara girman wurin biki da ma shagunan da aka kafa a filin biki, don haka ba kowa ne zai samu shiga bikin ba, abin da ya alamta cewa, duk da koma bayan da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, kasashen duniya na kokarin shiga kasuwar kasar Sin, don cin gajiyar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin. Musamman ma a halin yanzu da ake fuskantar manufar bangaranci da kariyar ciniki, da tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya da zuba jari ke fuskanta, kasuwar Sin mai salon bude kofa na samar musu da damammaki masu dimbin yawa. Abin lura shi ne, CIIE ta zama wata alama dake bayyana yadda Sin take gudanar da manufar bude kofa ga ketare. Bikin baje koli na wannan karo mafi girma da inganci ya kunshi ayyuka masu dimbin yawa na nunawa duniya niyyar kasar Sin na nacewa ga manufar kasancewar bangarori daban-daban a duniya da ingiza ciniki maras shinge. (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba