Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori masu adawa da juna na Sudan sun bayyana fatan kawo karshen rikicinsu
2019-10-16 11:05:37        cri
Gwamnatin riko na Sudan da kungiyoyi masu dauke da makamai, sun bayyana fatan kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana yi, suna masu bayyana tattaunawar da za a yi a Juba a matsayin wadda aka samar da ita a cikin gida.

Shugaban gwamnatin, Abdel Fattah Al-Burhan, ya ce tattaunawar za ta magance tushen abubuwna dake haifar da rikicin, yana mai cewa Juba wuri ne da ya dace gudanar da ita.

Ya ce a matsayinsu na shugabannin gwamnatin, suna bayyana cikkaken goyon bayansu ga tattaunawar da za ta kawo karshen matsalar al'ummar Sudan.

Shugaba Salva Kirr na Sudan ta kudu ne ya gabatar da bukatar ta shiga tsakanin bangarorin masu adawa, bayan shafe shekara ana takkadamar siyasa a kasar.

Alhadi Idris, shugaban kungiyar kawancen kungiyoyin adawa masu dauke da makamai ta Sudanese Revolutionary Front, ya ce kungiyarsa na ba batun zaman lafiya da ci gaban al'ummar Sudan muhimmanci, yana mai cewa tattauanwar ta Juba, za ta samar da kyakkyawar hanyar da bangarorin za su warware rikicinsu cikin ruwan sanyi.

Shi kuwa Abdalaziz Adam Halilu, shugaban kungiyar SPLM na bangaren arewacin kasar, cewa ya yi, bangarensa ya amince da Juba a matsayin wurin tattaunawar, tun da yunkurin Tarayyar Afrika ya gaza warware rikicin na Sudan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China