Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei na kasar Sin ya bada lambobin yabo ga matasan Nijeriya masu basira a fannin fasahar sadarwa
2019-07-05 09:55:18        cri

Kamfanin fasaha na kasar Sin Huawei, ya bada lambobin yabo ga matasan Nijeriya da suka nuna kaifin basirar da suke da shi a fannin fasahar sadarwa, yana mai kira da su yi amfani da basirar wajen raya kasarsu.

Yayin bikin mika lambobin yabo da kamfanin ya shirya a birnin Abuja ga matasa 3 na farko da suka yi nasara a zagayen karshe na gasar da kamfanin ya shirya ta 2018-2019 a farkon bana a kasar Sin, kamfanin ya ce manufarsa ita ce, dalibai su mallaki abubuwan da sana'ar fasahar sadarwa ke bukata ta hanyar kwarewa kan dabarun fasahohin sadarwa na zamani yayin da suke makaranta.

Matasan sun zamo zakaru ne a gasar musayar fasahar sadarwa ta duniya, wanda ya kunshi jami'o'i da kwalejojin nazarin fasahar sadarwa da kamfanin ya amince da su.

A cewar shugaban kamfanin a Nijeriya, Tank Li, dalibai 13,000 daga jami'o'i sama da 30 ne suka shiga gasar.

Tank Li ya ce bayan zagaye 3 na gasar, daya a matakin kasa, daya a matakin kudancin hamadar Sahara dake Afrika, daya a mataki na duniya, 'yan Nijeriya 6 ne suka zamo zakaru a matakin kasa da na kudancin hamadar Sahara dake nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China