Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban Amurka ya yi kira ga kawayen kasar da su dakatar da hadin kai da Huawei
2019-09-06 19:44:27        cri

Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, ya kai ziyara a kwanan baya kasar Iceland, inda ya shaidawa manema labarai cewa, kasashen biyu za su tattauna kan yadda Amurka za ta gina tsarin yanar gizo na 5G, kuma Amurka za ta yi kira ga kawayenta, ciki hadda Iceland, da su dakatar da hadin kai da kamfanin fasaha na kasar Sin wato Huawei.

Game da wanann batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Juma'a cewa, matakin da Amurka ke dauka, tamkar manufar kama karya, da mayar da batun ciniki a matsayin siyasa ne, kuma ko kadan Sin ba za ta yarda da hakan ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China