Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bude bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2
2019-10-28 11:23:00        cri
A ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa, za a bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu, wanda za a kammala a ranar 10 ga watan Nuwamba.

A wannan karo, akwai yankunan nune-nune guda 7 da za su hada da yankin cinikin ba da hidima, yankin motoci, yankin na'urori, yankin kimiyya da fasaha, yankin jin dadin zaman rayuwa, yankin na'urorin ba da jinya, yankin kiwon lafiya da kuma yankin amfanin gona. Idan aka kwatanta da bikin karo na farko, za a iya ganin cewa, an kara aikin kiwon tsoffaffi cikin bikin na wannan karo, da kuma kafa yankin nune-nune a waje, inda za a iya gwajin motoci maras matuki da dai sauransu.

Bugu da kari, bisa labarin da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fidda a baya, an ce, akwai kamfanoni sama da dubu 3 daga kasashe kimanin 150 da za su halarci biki na wannan karo. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China