Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2 zai fi karo na farko
2019-10-29 12:42:48        cri

Za a bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2 a mako mai zuwa, kuma bikin na wannan karo zai fi na baya ta fannonin kasaita da ma inganci.

Bana, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2 zai kasu gida uku, ciki har da bikin nune-nune na kasa da kasa, bikin nune-nune na kamfanoni da harkokin kasuwanci, da kuma taron dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin kasa da kasa na Hongqiao.Ya zuwa yanzu, akwai kasashe 64 da kungiyoyin kasa da kasa 3 da za su halarci bikin nune-nunen na kasa da kasa, domin nuna sakamako da ci gaban da suka samu a fannin zuba jari da harkokin ciniki.

A bikin nune-nunen kamfanoni da harkokin kasuwanci kuma, za a kafa yankunan nune-nune guda 7 da za su hada da yankin nuna cinikin ba da hidima, yankin nuna motoci, yankin nuna na'urori, yankin nuna kimiyya da fasaha, yankin nuna harkokin jin dadin zaman rayuwa, yankin nuna na'urorin ba da jinya da harkokin kiwon lafiya, da kuma yankin nuna amfanin gona. Kuma, a halin yanzu, akwai kamfanoni sama da dubu 3 daga kasashe kimanin 150 da za su halarci bikin na wannan karo, adadin da ya wuce bikin karo na farko.

A wannan karo, an kyautata yankunan nune-nune da kuma inganta ingancin kayayyakin da za a nuna. Yanzu, kamfanoni sama da 250 dake cikin jerin fitattun kamfanoni guda 500 na kasa da kasa sun riga sun kulla yarjejeniyar shiga bikin. Kuma adadin sabbin kayayyaki da sabbin fasahohi da za a nuna a yayin bikin karo na biyu zai wuce adadin na bikin karo na farko. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China