Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci kasashen Afrika su magance matsalolin ta'addanci da sauyin yanayi
2019-10-08 10:32:40        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen Afrika su magance matsalolin ta'addanci da sauyin yanayi domin wanzar da tsaro da zaman lafiya.

Yayin wata muhawara ta Kwamitin Sulhu na MDD kan matakan diflomasiyya da na kare rikici da yin sulhu a Afrika, Antonio Guterres ya ce ta'addanci barazana ce dake karuwa a fadin nahiyar Afrika, wanda kuma ke mummunan tasiri kan zaman lafiya da tsaro.

Ya ce a yankin Sahel, kungiyoyin 'yan ta'adda kan kai hare-hare kan dakarun yankin har ma da na kasa da kasa. Sannan rikici na bazuwa a kasashen dake kan gabar tekun Guinea.

Ya ce a Nijeriya kuwa, BH da wani tsagi nata, sun addabi al'ummomin tare da farwa jami'an tsaro, duk da kokarin sojojin kawancen kasashe.

Antonio Guterres ya nemi tallafin ayyukan soji, ciki har da shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika dake aiki a Somalia da dakarun kawancen kasashen yankin Sahel 5 da kuma dakarun kawance na kasashen wajen yaki da BH.

Har ila yau, ya ce magance sauyin yanayi, matakin kariya ne mai muhimmanci, domin matsalolin yanayi da suka hada da fari da ambaliya da sauyin yanayin saukar ruwar sama, na da alaka da batutuwan siyasa da zamantakewa da tattalin arziki, don haka, dole ne a rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli domin kare matsalolin da za su haifar ga dawwammen ci gaba da wanzuwar tsaro a fadin Afrika, tare da kara kaimi wajen tallafawa kasashen da matsalar ta fi shafa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China