Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi kira ga kasa da kasa da su kara zuba jari a kasashen dake yankin manyan tafkuna
2019-10-04 15:45:29        cri
A jiya ne, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya yi kira ga kasa da kasa da su kara zuba jari a kasashen dake yankin manyan tafkuna a fannonin hadin gwiwa, da kiwon lafiya, da ba da ilmi da sauran ayyukan more rayuwa, ta yadda za a samar da ayyukan yi da kyautata rayuwar jama'ar yankin.

Zhang Jun ya bayyana hakan ne a wannan rana, yayin da yake jawabi a zaman kwamitin sulhun MDD kan batun yankin Great Lakes, yana mai cewa, bunkasuwa za ta iya warware dukkan matsaloli. Ya ce talauci da rashin samun ci gaba, su ne suka kawo matsala a yankin manyan tafkuna, kuma hanya guda ta daidaita matsalar, ita ce samun bunkasuwa mai dorewa.

Zhang Jun ya kara da cewa, Sin ta yi kokarin shimfida zaman lafiya a yankuna daban daban, da ma shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya a wannan yanki, da samar da gudummawar aikin soja tare da nuna goyon baya ga yunkurin samun zaman lafiya a kasashen yankin. Sin za ta ci gaba da kokarin raya karfin kasashen yankin, da samar musu da gudummawa a fannonin ayyukan more rayuwa, da aikin noma, da kiwon lafiya da sauransu, ta yadda za a samar da zaman lafiya ta hanyar samun bunkasuwa. Kana Sin za ta sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka a tsakaninta da kasashen yankin, da kara yin mu'amalar al'adu a tsakanin jama'arsu, da raya alakar imani da juna da hadin gwiwa da mu'amalar al'adu, hakan zai taimaka wajen shimfida zaman lafiya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China