Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin kasar Sin ya kammala aikin samar da talabijin na zamani a kauyuka 1,000 a Najeriya
2019-10-30 10:03:26        cri

Babban kamfanin samar da fasahar talabijin ta zamani na kasar Sin StarTimes, ya kammala aikin samar da talabijin mai amfani da tauraron dan adam a kauyuka 1,000 a Najeriya, da nufin taimakawa al'ummomin yankunan karkara samun damar cin gajiyar amfani da talabijin na zamani a kasar mafi yawan al'umma ta yammacin Afrika.

A yayin gagarumin biki da aka gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya, don murnar kammala aikin, gwamnatin Najeriya, da wadanda suka ci gajiyar shirin, sun yaba da aikin wanda ya kasance daya ne daga cikin muhimman yarjejeniyoyin da aka cimma a taron kolin Johannesburg na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) a shekarar 2015, inda a lokacin ne gwamnatin kasar Sin tayi alkawarin samar da talabijin mai amfani da tauraron dan adam ga kauyukan Afrika 10,000. Baki daya, kimanin magidanta 20,000 mazauna yankunan karkara a Najeriya ne suka amfana daga shirin.

Shirin wanda gwamnatin Sin ta dauki nauyinsa, kamfanin StarTimes ya kaddamar da aikin ne a ranar 14 ga watan Janairu, kowane daga cikin kauyuka 1,000 da aka zaba a Najeriya sun samu seti biyu-biyu na na'urar dake haska hotunan talabijin mai amfani da hasken rana da seti akwatin talabiji wanda girmansa ya kai inch 32 guda daya.

Odebunmi Dokun, dan majalisar dokokin Najeriya kana shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin kasar, ya ce kammala aikin wani muhimmin mataki ne da zai kara karfafa huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Najeriya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China