![]() |
|
2019-10-25 10:37:28 cri |
Gwamnan jiihar Legas dake Najeriya Babajide Sanwo-Olu, ya ce aikin tashar ruwan teku mai zurfi ta Lekki wanda kasar Sin ta zuba jarin dala miliyan 629, aikin tashar ruwan teku mai zurfi irinsa na farko ne a Najeriya, wanda zai bunkasa tattalin arzikin yankin.
Cikin yanayin farin ciki gwamna Sanwo-Olu ya bayyana a lokacin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar fara aikin wanda aka gudanar a ranar Laraba, ya ce aikin ya kasance a matsayin gagarumin cigaba ga bangaren samar da kayayyakin more rayuwa a jihar, ya kara da cewa, sanya hannu kan yarjejeniyar fara aikin ya kawar da duk wani shakku da aka jima ana yinsa game da yiwuwar gudanar da aikin tashar tekun na Lekki.
A cewarsa, idan aikin ya kammala zai kara habaka tattalin arzikin jihar Legas kuma zai sanya jihar cikin manyan yankuna masu karfin tattalin arziki a duniya.
Ya ce wannan wani sabon tushe ne ga jihar Legas, an cimma gagarumar nasarar kawo sauye sauye a burin da ake neman cimmawa na bunkasuwar tattalin arziki a karni na 21.
Gwamnan yana fatan sakamakon aikin zai haifarwa jihar bunkasuwar tattalin arziki.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China