Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron matasa masu nazarin kimiyya da fasaha a kasar Sin
2019-10-26 17:05:06        cri
A yau Asabar, aka bude taron matasa masu nazarin kimiyya da fasaha na duniya na shekarar 2019 a garin Wenzhou dake gabashin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude taron, inda ya ce, yanzu haka ana ganin farawar sabon zagayen juyin juya hali a fannin kimiyya da masana'antu, kana masu jagorantar juyin juya halin matasa ne. Saboda haka, kasashe daban daban na da buri na bai daya na ganin matasa za su kara musayar ra'ayoyinsu a fannonin kimiyya da al'adu, da neman kirkiro sabbin fasahohi, da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Shugaban na kasar Sin ya ce yana fatan mahalarta taron za su yi koyi da juna, da musayar tunaninsu, da sada zumunta, tare da kulla huldar hadin gwiwa da juna, ta yadda za a baiwa matasa masu nazarin kimiyya da fasahar damar cika burikansu, da sanya sabbin fasahohi taimakawa raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, tare da kokarin tabbatar da wata makoma mai haske ga daukacin bil Adama.

Masu halartar taron kimanin wasu 800 sun hada da shehunan malaman da suka taba samun lambobin yabo na Nobel, da shahararrun matasa masu nazarin kimiyya da fasaha, gami da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa masu alaka da kimiyya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China