Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya taya murnar bude taron "Fahimtar kasar Sin"
2019-10-26 17:04:18        cri
A yau Asabar aka bude taron kasa da kasa mai taken "Fahimtar kasar Sin" a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, inda shugaban kasar mista Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude taron.

A cewar shugaban, duk da cewa yunkurin dukulewar tattalin arzikin duniya na fuskantar wasu kalubale, ba za a iya mai da agogon baya dangane da wannan yunkuri ba, domin a wannan zamanin da muke ciki, moriyar kasashe daban daban na kara gauraya da juna, kana makomarsu na kara zama irin na bai daya, yayin da jama'arsu ke da buri daya, wato neman jin dadin zaman rayuwa.

Shugaban ya ce, kasar Sin ta amfana daga tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya, sa'an nan tana kokarin samar da gudunmowa don ganin kowa ya amfana bisa tsarin. Kasar Sin, a cewar shugaba Xi, za ta nace ga manufar neman ci gaba tare da tabbatar da zaman lafiya, da kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe da zummar amfanawa dukkan bangarori. Har ila yau, ya ce kasar za ta taimaka ga kokarin kyautata tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya, ta yadda zai dace da manufofin bude kofa, da amfanawa kowa, da hakuri da juna, gami da samun daidaito, ta yadda za a yi amfani da wannan tsari wajen haifar da alfanu ga jama'ar kasashe daban daban. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China