Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya gana da wakilan dake halartar taron fahimtar kasar Sin
2019-10-25 20:14:11        cri
A yau Jumma'a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan kasashen waje dake halartar taron fahimtar kasar Sin.

Yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana fatan, wakilan za su fahinci kasar Sin a zahiri, ta hanyar kara zurfafa musaya da kasar ta Sin.

Taron fahimtar kasar Sin wanda za a gudanar daga yau Jumma'a 25 – 27 ga wata a Guangzhou dake kudancin kasar Sin, zai hallara 'yan siyasa da masu tsara dabaru da masana da 'yan kasuwa sama da talatin daga sassan duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China