Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi:Kafin Yin Tambaya, CNN Ya Riga Ya Shirya Amsa
2019-10-28 15:53:59        cri
An gano gawawwakin wasu 'yan Asiya 39 a cikin wata babbar mota mai kankara a kasar Birtaniya, wannan shi ne labari mafi janyo hankalin mutanen duniya da ya abku a wannan makon da muke ciki. Sai dai kafin a tabbatar da asalin mamatan, da kuma dalilin da ya sa suka rasa rayukansu, kafar watsa labaru ta CNN ta kasar Amurka ta riga ta nuna cewa wadannan mutane 'yan kasar Sin ne, har ma wani wakilinta ya tambayi ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, cewa "Me ya sa Sinawa ke son barin kasar Sin ta wannan hanya mai matukar hadari, yayin da kasar ke murnar cika shekaru 70 da kafuwarta?"

Daga bisani, zuwa ranar 27 ga wata, an samu ci gaba wajen binciken ta'assar da ta abku, inda kamfanin dillancin labarai na kasar Vietnam ya watsa labarin cewa, ko da yake yanzu ba a iya tabbatar da cewa dukkan mutanen 39 da suka mutu 'yan kasar Vietnam ne, amma a kalla dai wasu iyalai 24 daga kasar Vietnam sun riga sun sanar da bacewar 'yan iyalansu a nahiyar Turai ga 'yan sanda.

Wannan lamari ya nuna yadda kafofin watsa labaru na kasashen yamma suke nuna son zuciya yayin da suke watsa labarai game da kasar Sin. A ganinsu, duk wani matakin da kasar Sin ta dauka ba daidai ba ne. Sa'an nan dalilin da yasa haka, shi ne domin wadannan kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna raba kafa dangane da ra'ayinsu a fannin siyasa. (Bello Wang, ma'aikacin sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China