Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin kasar Sin za ta taimaka wajen samun kyakkyawar makoma a Internet
2019-10-21 14:08:24        cri

In babu tsaro a Internet, to babu tsaron kasa. Ko wace irin fasaha ta kawo wa mutane dama tare kuma da barazana. Yayin da muke jin dadin samun ci gaba da wadata da kuma saukin samun bayanai ta hanyar Internet, muna fuskantar barazana da kalubale. A shekarun baya, a kan samu barkewar hare-haren masu kutsen Internet, da bayyana abubuwan sirri da suka shafi rayuwar mutum, leken asiri ta Internet, da kuma ta'addanci kan Internet. Wasu kasashe sun yi danniya kan Internet, da ci zalin fasahar Internet ta sauran kasashe da masana'antunsu, lamarin da ya tsananta damuwar kasashen duniya.

Samun kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam kan Internet ya dace da zamani, wanda kuma zai cika burin kasashen duniya. Abu mai muhimmanci wajen samun kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam kan Internet shi ne, tsayawa tsayin daka kan tafiyar da harkoki masu ruwa da tsaki cikin hadin gwiwar sassa daban daban kuma ta hanyar yin shawarwari tare, a kokarin samun amfanar kowa, haka kuma a tsaya tsayin daka kan ganin al'ummomin kasa da kasa sun yi shawarwari wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa, in ba haka ba, sakamakon ci gaban Interent ba zai amfana wa 'yan Adam ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China