Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban Najeriya zai jagoranci tawagar AU don sanya ido a zaben Mozambique
2019-10-14 10:49:18        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan zai tafi Maputo, babban birnin kasar Mozambique domin jagorantar tawagar kungiyar AU dake sanya ido kan zaben kasar.

Kungiyar Pan-Afirka mai mambobin kasashen Afrika 55 ne ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, cewa tsohon shugaban na Najeriya yana jagorantar tawagar AU ta sanya ido kan zabe (AUEOM) mai mambobi 44 don sanya ido a zaben na kasar Mozambique. Tawagar wacce ta kunshi jakadu daga kwamitin wakilai na dindindin a kungiyar ta AU, da mambobin majalisar dokoki ta Pan-Africa, da jami'an hukumomin zabe, da kungiyoyin fararen hula, da 'yan jaridu da kuma kwararru a fannin zabe,

Sanarwar ta ce, tura tawagar ta AUEOM zuwa Mozambique, ya nuna kokarin da AU ke yi wajen tabbatar da samun sahihi kuma ingantaccen zabe, cikin lumana da kwanciyar hankali a kasashen Afrika ta hanyar samar da jami'an da zasu nazarci yadda aka shirya zaben da yadda yanayin siyasar kasar ke gudana.

Jonathan, ana sa ran zai tattauna da masu ruwa da tsaki a harkokin zaben kasar ta Mozambique, wanda ya hada da shugaban hukumar zaben kasar Mozambique, da shugabannin jam'iyyun siyasar kasar, kungiyoyin fararen hula, shugabannin kungiyoyin kasa da kasa dake sanya ido a zaben, da kuma jami'an hukumomin diflomasiyya dake kasar gabanin fara zabukan. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China