Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mozambique tana bukatar dala biliyan 3.2 don sake gina kasar bayan bala'in guguwa
2019-05-15 11:54:26        cri
Kasar Mozambique tana bukatar kimanin dala biliyan 3.2 domin gudanar da ayyukan sake gina kasa a yankin tsakiya da arewacin kasar inda bala'in mahaukaciyar guguwa ta Idai da ta Kenneth ya daidaita, gwamnatin kasar ta sanar da hakan ne a lokacin taron majalisar ministocin kasar na mako mako a Maputo.

Kakakin gwamnatin kasar Ana Comoana, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai cewa an samu alkaluman ne a rahoton tantace barnar da bala'in ya haddasa wanda hukumomin gwamnatin kasar da wasu hukumomi masu zaman kansu suka binciko, wanda ake saran za'a gabatar da shi a taron neman gudunmowa wanda za'a gudanar a Beira a karshen watan Mayu.

Sakamakon afkuwar bala'in mahaukaciyar guguwa ya sa gwamnatin kasar Mozambiq ta rage hasashenta na karuwar (GDP) daga kashi 4.7% zuwa kashi 2.5%. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China