Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mozambique ta kaddamar da shirin tallafawa mata
2019-08-29 11:31:04        cri
Ma'aikatar kula da jinsi, yara da walwalar jama'a ta kasar Mozambique (MGCAS), ta kaddamar da wani shiri a Maputo, game da bunkasa yanayin tattalin arzikin matan kasar.

An tsara shirin ne da nufin rage matsalolin da suka shafin karancin ilmi, da rashin samun damammakin karbar rancen kudade, da fasahohin zamani da suka shafi bunkasa sana'o'in dogaro da kai dake shafar mata, musamman mazauna yankunan karkara.

Mozambique tana bukatar gaggauta zuba jari wajen bunkasa tattalin arzikin mata ta hanyar samar musu da sana'o'in dogaro da kai kasancewar matakin babban jigo ne na raya tattalin arzikin kasar, wakilin bankin raya ci gaban kasashen Afrika dake Mozambique, Pietro Toigo, shi ne ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da shirin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China