Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya bukaci a kyautata aikin samar da magungunan gargajiya
2019-10-25 14:37:56        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umarni ga aikin samar da magungunan gargajiya na kasar a kwanakin baya, inda ya ce likitancin gargajiya na kasar Sin na kunshe da ra'ayin kiwon lafiya mai tarihi, gami da fasahohin da aka samu daga gwaje-gwajen da aka yi cikin shekaru fiye da dubu daya da suka wuce, saboda haka ilimi game da likitancin gargajiya na kasar na da daraja matuka. Sa'an nan shugaban ya bukaci a gaggauta zamanantar da aikin samar da magungunan gargajiya, gami da kokarin sayar da su a kasuwannin duniya.

An saurari umarnin shugaban ne a wajen taron likitanci da magungunan gargajiya na kasar Sin da ya gudana a yau Jumma'a, a birnin Beijing na kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China