Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar bude babban taron IEC karo na 83
2019-10-21 21:17:37        cri
An kaddamar da bikin bude babban taron hukumar kasa da kasa mai kula da ingancin kayayyakin laturoni (IEC) karo na 83 a yau Litinin a birnin Shanghai na kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuto aike da wasikar murnar bude taron.

A cikin wasikar, Xi ya nuna cewa, a yanzu haka kiyaye muhalli da tabbatar da bunkasuwa mai dorewa shi ne muradun daukacin bil Adam, wasu sabbin fasahohi, ciki har da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, da ta manyan bayyanai, da fasahar 5G da sauransu suna samun ci gaba tare da fasahohin samar da wutar lantarki da sabbin makamashi, da motoci masu amfani da wutar lantarki da makamantansu, don haka, akwai bukatar tsara da amfani da ma'aunin kasa da kasa a wadannan fannonin, da karfafa hadin kan kasa da kasa a fannonin.

Haka zalika Xi ya jaddada cewa, kasarsa na son hada kai da kasashe daban daban, don kara kyautata tsarin ma'auni da tsarin tafiyar da karkokin kasa da kasa, ta yadda ma'aunin zai kara taka muhimmiyar rawa a harkokin cinikayyar kasa da kasa da ayyukan gudanarwa na duniya.

A shirye kasar Sin ta ke, ta hada kai da sauran kasashe, don ci gaba da inganta tsarin tsai da ma'aunai, ta yadda ma'aunai za su taka rawa a harkokin cinikayar kasa da kasa da tafiyar da harkokin duniya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China