2019-10-24 11:13:41 cri |
Cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana tsayawa kan manufar samun ci gaba ta hanyar kirkiro sabbin fasahohi, da neman samun daidaituwa, da kare muhalli, da bude kofa ga ketare, da kokarin amfanawa kowa. A cewarsa, kasar Sin na neman raya tattalin arziki tare da tabbatar da ingancinsa, gami da kokarin aiwatar da manufar ajandar samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030. A sa'i guda, kasar Sin tana kokarin zurfafa hadin gwiwarta tare da sauran kasashe masu tasowa, da neman daidaita shawarar kasar ta "Ziri Daya da Hanya Daya" da ajandar samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030, don samar da gudunmowa ga yunkurin kasashe daban daban na tabbatar da samun ci gaba mai dorewa. Shugaban kasar Sin ya ce, yana fatan ganin bangarori mahalartar taron za su lalubo hanyar da za a bi don cimma burikan da jama'ar kasashe daban daban suka sanya a gaba, da sanya kasashe daban daban samun ci gaba tare, don tabbatar da makoma mai haske ta bai daya ga daukacin bil Adama.
Wannan taro na tattauna batun samun ci gaba mai dorewa shi ne irinsa na farko, masu karbar bakuncin taron su ne cibiyar nazarin dabarun samun ci gaba karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, da gwamnatin birnin Beijing, da wasu hukumomi masu ruwa da tsaki na MDD. Sa'an nan makasudin taron shi ne tattauna matakan da za a iya dauka don aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030, da kuma fasahohin da aka samu a wannan fanni. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China