Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birane 39 a Sin na amfani da jirgin kasa mai tafiya karkashin kasa
2019-10-25 10:04:21        cri

Mai magana da yawun hukumar zirga-zirga ta kasar Sin Wu Chungeng ya nuna a jiya Alhamis cewa, ya zuwa yanzu, birane 39 a kasar na amfani da jirgin kasa mai tafiya a karkashin kasa, yawan layin dogo ya kai kilomita 5800, yawan fasinjojin dake amfani da wannan jirgi ya kai biliyan 21.3 a shekarar 2018, hakan ya sa wadannan adadi ke matsayin farko a duniya. Ban da wannan kuma, wasu ma'auni na ingancin ayyukan jirgi na sahun gaba a duniya, sannan kuma ana tafiyar da aiki lami lafiya, ba tare da samun hadari mai tsanani ba a wannan fanni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China