Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jiragen kasa na Sin sun yi jigilar fasinjoji biliyan 2.8 cikin farkon watanni 9 na bana
2019-10-22 11:19:40        cri

 

Yawan fasinjojin da suka ji bulaguro ta jiragen kasa na kasar Sin sun kai biliyan 2 da miliyan 800 a watanni taran farko na wannan shekara, adadin da ya karu da kashi 9.4% idan an kwatanta da makamantan lokacin bara, hukumar sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ta sanar da hakan.

Kimanin fasinjoji biliyan 1.73 sun yi tafiye tafiye ta jiragn kasa masu saurin tafiya tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar wannan shekara, adadin da ya karu da kashi 15.3% idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.

A cikin wannan wa'adin, kimanin jiragen kasa 8,538 ne suka gudanar da aikin jigilar fasinjojin a kowace rana kuma daga cikin adadin jiragen kasa masu saurin tafiya sun kai kashi 71.6%, sai kuma jiragen kasan masu saurin tafiya samfurin Fuxing kashi 12% daga cikin adadin.

Hukumar sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ta bullo da tsarin sayen tikiti ta hanyar intanet na gwaji, da nufin saukaka tsarin sayen tikitin, da kuma aiwatar da tsarin sayen tikiti cikin sauki ga tsoffi da kananan yara da nufin samar da ingantaccen yanayin ga fannin zirga zirga. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China