Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi gwajin tafiyar sabbin jiragen dake karkashin kasa na kasar Sin cikin nasara
2019-06-20 13:50:37        cri
Bisa labarin da kamfanin Sifang na CRRC na kasar Sin ya bayar, an ce, an yi gwajin tafiyar sabbin jiragen dake karkashin kasa guda shida da kamfanin ya kera cikin nasara. An yi amfani da sabbin fasahohi wajen kera irin jiragen dake karkashin kasa, ana kiransu da sunan "jiragen dake karkashin kasa na nan gaba".

An ce, za a rage nauyin jiragen dake karkashin kasa da kuma rage yawan wutar lantarki da za a yi amfani da ita wajen yin tafiya. Jirgin marar matuki ne, kuma saurin tafiyarsa zai kai kilomita 140 a kowace awa. Ana iya duba shafin internet, da kallon bidiyo, da samun labarai, da kallon telebijin a kan tagar jiragen. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China