Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron baje kolin kayayyakin fasaha na kasa da kasa a Sin
2019-09-06 09:55:53        cri

An bude taron baje kolin kayayyakin kimiyya da fasaha karo na 7, jiya Alhamis a birnin Mianyang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin.

Taron na yini 4, ya ja hankalin kamfanonin fasaha 687 daga fadin duniya, ciki har da Microsoft da Panasonic, wadanda za su baje kayayyakin fasaha na zamani sama da 10,000, a fannonin fasahar adana bayanai da na kwaikwayon tunanin dan Adam da na kera keren kayayyaki.

Austria, kasar dake matsayin babbar bakuwa, ta hada kamfanonin fasaha sama da 10, domin halartar bikin.

Ministan sufuri da kirkire kirkire da fasaha na Austria, Andreas Reichhardt, ya ce yana fatan wannan zai zama mafarin kulla dangantakar cinikayya mai inganci da za ta amfanawa bangarorin biyu.

Mataimakin shugaban ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, Wang Xi, ya ce ana sa ran baki da kamfanoni mahalarta taron, su karfafa hadin gwiwa da tuntubar juna ta hanyar baje kolin.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China