Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: An kammala taron baje kolin kayan manyan fasahohi tare da sanya hannu kan karin kwangiloli
2019-09-09 10:09:21        cri

An kammala taron baje kolin kayan manyan fasahohi na Mianyang karo na 7, tare da sanya hannu kan karin kwangiloli 105, wadanda darajar su ta kai kudin Sin yuan biliyan 92.38, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 13.2.

An dai gudanar da wannan baje koli ne a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Alkaluma sun tabbatar da cewa, jimillar kudin kwangilolin da aka sanyawa hannu yayin baje kolin na wannan karo, sun haura na bara da kusan yuan biliyan 2. A cewar masu shirya baje kolin, cikin wadannan kwangiloli, hadda wasu 39, wadanda kowannen su zai kunshi jarin da ya haura yuan miliyan 500.

An dai baje kolin manyan fasahohi da suka haura 10,000, ciki hadda na samar da bayanai ta na'urorin zamani, da na sarrafa kayan ayyuka, da na fasahar kwaikwayon tunanin bil Adama.

Bikin ya samu halartar wakilai daga jami'o'i 20, da masana, da kamfanonin kere keren manyan fasahohi 687 daga sassan duniya daban daban, ciki hadda na kamfanonin Amazon, da Microsoft da Panasonic.

Ana gudanar da wannan biki na baje koli ne sau daya a duk shekara, tun daga shekarar 2013. Ya zuwa yanzu kuma, ya jawo jarin da yawan sa ya kai sama da kudin Sin yuan biliyan 645. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China