Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon firaiministan Habasha ya bukaci kasashen Afrika su rungumi fasahar samar da abinci
2019-08-17 15:51:53        cri
Tsohon firaiministan kasar Habasha ya shawarci kasashen Afrika su zuba jari a fanninn sabbin fasahohin aikin gona na zamani domin kaucewa tafka hasara a sakamakon matsalar sauyin yanayi da kuma magance matsalar karancin abinci wanda ke shafar kasashe da dama a nahiyar.

Hailemariam Desalegn, wanda shi ne sabon shugaban hukumar hadin gwiwar raya aikin gona na Afrika wato (AGRA), ya bukaci a tabbatar da hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki na hukumomin gwamnati da masu zaman kansu domin bada fifiko wajen yin bincike da musayar kwarewa game da yadda za'a shigar da fasahohin zamani a fannin aikin gona.

Ya bayyana hakan ne a Nairobi jim kadan bayan an tabbatar da shi a matsayin wanda zai shugabanci hukumar, ya ce a duk fadin duniya, samar da abinci shi ne muhimmin batu na ajandar raya cigaban gwamnatoci, yarjejeniyar Maputo ta bukaci kasashen Afrika da su ware kaso 10 bisa 100 na kasafin kudadensu ga fannin aikin gona, kuma su zuba kaso mafi yawa a fannin fasahohin zamani domin cimma wannan buri.

Desalegn ya ce, akwai bukatar daukar matakan gaggawa wajen samar da fasahohin zamani don gano hanyoyin amfani da nau'ikan irin shukawa wadanda suke iya jure fari, wadanda za su dace da yanayin muhallin aikin gona, wadanda kuma za su samar da amfanin gona mai yawa domin rage tafka hasara. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China