Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyar mai mulkin Zambia ta kaddamar da yaki da masu batancin ta shafukan sada zumunta
2019-06-04 09:42:13        cri
A jiya Litinin jam'iyyar gwamnati mai mulkin kasar Zambia ta kaddamar da shirin sanya ido da kuma bibiyar masu aikata kalaman batanci ta shafukan sada zumunta na zamani wanda magoya bayan jam'iyyu ke aikatawa.

Davies Mwila, sakatare-janar na jam'iyyar Patriotic Front (PF), ya bayyana hakan a lokacin gudanar da taron kwamitin tsakiya na kolin jam'iyyar a ranar 2 ga watan Yuni, da nufin lalibo bakin zaren magance matsalar kalaman batanci da magoya bayan jam'iyyu ke aikatawa.

Ya ce kirkiro kwamitin sanya ido game da shafukan sada zumuntan zai taimaka wajen yaki da masu aikata laifin kalaman batanci ta kafafen sada zumuntar, kuma ba za'a laminci duk wani batu da ya shafi cin mutunci ko cin zarafi a jam'iyyar ba.

Tuni dai hukumar kolin jam'iyyar ta umarci dukkan shugabannin larduna da su dinga tuntubar babbar sakatariyar jam'iyyar ta kasa domin su sanya ido tare da yin rejistar dukkan shafukan sada zumunta da aka kirkira a matakan gundumomi da na larduna. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China