Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zambia za ta amfana daga kara hadin gwiwa da Kasar Sin
2019-07-30 09:51:09        cri
Kungiyar masu inganta harkokin cinikayya da kasuwanci ta Chingola, ta ce Gwamnatin Zambia na bada muhimmanci sosai ga hadin gwiwarta da kasar Sin, lamarin da ta ce, zai amfani al'ummar kasar ta hanyar bunkasar tattalin arziki.

Shugaban kungiyar Fred Musonda, ya ce Zambia na amfana daga ci gaban tattalin arzikin Kasar Sin, ta hanyar ingantuwar harkokin cinikayya tsakaninta da kasar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Zambia da ta karfafa hadin gwiwa da kasar Sin karkashin Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

A cewar Fred Musonda, hadin gwiwa karkashin shawarar zai ba Zambia damar raya ababen more rayuwa na kasar, wanda zai kai ga bunkasar tattallin arziki.

Har ila yau, Peter Daka mazaunin garin Chingola, ya ce shawarar Ziri Daya da Hanya Daya muhimmin shiri ne da zai amfani Zambia da nahiyar Afrika da ma sauran sassan duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China