Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa miliyan 105 ne suka yi yawon bude ido yayin hutun bikin tsakiyar kaka
2019-09-16 10:22:11        cri

Ma'aikatar raya al'adu da yawon bude ido ta kasar Sin, ta ce jimilar Sinawa miliyan 105 ne suka yi bulaguro a fadin kasar, yayin hutun kwanaki 3 na bikin tsakiyar kaka na bana, da aka fara daga ranar Juma'ar da ta gabata.

Ma'aikatar ta ce adadin ya nuna karuwar kaso 7.6 a kan na makamancin lokacin bikin a bara.

Alkaluman da ma'aikatar ta fitar, sun nuna cewa kudin shigar da aka samu daga yawon bude ido a cikin gida yayin hutun, ya kai yuan biliyan 47.28, kwatankwacin dala biliyan 6.7, wanda ya karu da kaso 8.7 a kan na bara.

Yayin hutun, an gudanar da shirye-shirye da dama dake nuna muhimmancin raya zumunci da kishin kasa da al'adun Sinawa na gargajiya a fadin kasar.

Ana gudanar da bikin tsakiyar kaka ne ta hanyar sada zumunci tsakanin iyalai da kallon wata da cin wainar wata da sauran wasu al'adu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China