Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na kara bunkasa amfani da naurori wajen tattara kudaden harajin manyan hanyoyin mota
2019-08-19 11:17:17        cri

Mahukuntan kasar Sin sun bayyana aniyar su, ta fadada samar da na'urorin zamani wadanda ake amfani da su wajen tattara kudaden harajin ababen hawa, a manyan titunan mota dake sassan kasar. Ya zuwa karshen shekarar nan ta bana, kasar na fatan ajiye wadannan na'urori cikin motocin da suka yi rajista da yawansu ya kai kaso 80 bisa dari a kasar.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta tanaji na'urorin tattara haraji na zamani ko ETC a takaice, wadanda yawan su ya kai miliyan 107, kana ana hasashen yawan masu amfani da su zai karu zuwa miliyan 180 nan da karshen wannan shekara.

An kuma tanaji rangwamen kaso 5 bisa dari ga masu ababen hawa dake amfani da na'urorin domin yayata amfani da su.

Matakin dai, wani bangare ne na kara inganta amfani da sashen sufuri ta hanyoyin mota, da kuma rage tsadar hidimomi da ake samarwa ta wannan hanya. Ana kuma fatan hakan zai share fagen kawar da dukkan tashoshin karbar harajin ababen hawa a manyan tagwayen hanyoyin da ke ratsa lardunan kasar nan da karshen shekara.

Wasu alkaluman bayanai da cibiyar bincike ta Qianzhan dake birnin Shenzhen ta fitar sun nuna cewa, daga watan Oktoban shekarar 2015 lokacin da aka kaddamar da amfani da na'urorin ETC, ya zuwa karshen shekarar 2018, tsarin ya samar da hidimomi ga direbobi na jimillar sa'o'i miliyan 52, daidai da awon makamashin da ake konawa har tan 347,000. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China